Saturday, 10 September 2016

Karya ka ke yi Oshiomole-Kwamishinan Jihar Rivers

– Dakta Austin Tam-George ya karyata maganar Oshiomole na cewa Gwamnonin Jihar Rivers da Delta sun yi hayar tsageru domin murgude zaben Jihar Edo

– Tam-George yace ba abin da ya hada Gwamna Wike da tsagerun na Naje-Delta kmar yadda Oshiomole ya fada

– Gwamna Adams Oshiomole ya zargi Gwamna Nyesom Wike na Rivers Da Ifeanye Okowa na Delta da hayar tsageru kusan 8,000 militants domin murde zaben Jihar Edo

Wike

 

 

 

Kwamishinan watsa labarai na Jihar Dakta Austin Tam-George ya musanya zargin da Gwamna Adams Oshiomole yayi ga Gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike da ma Gwamna Ifeanyi Okowa na Delta na cewar sun yi hayar tsageru domin tada rikici da murde zaben Gwamnan Jihar Edo. Dakta Tam-George yace karyar banza ce kawai Gwamnan yayi da yake cewa Gwamna Wike da danuwan sa sun hada kudi har Naira biliyan biyu domin murde zabe da sunan PDP.

KU KARANTA: APC za ta murde zaben Jihar Edo-Inji Gwamna Fayose

Dakta Tam-George ya bayyanawa wa NAIJ.com cewa Gwamna Wike bai bada wata gudumawa ba wajen ganin an murde zaben Jihar Edo. Kuma ya ce Gwamna Wike ba sa da wata alaka da tsagerun yankin da ma duk fadin Kasar nan. Kwamishinan yace Gwamnan na Jihar Rivers yayi abin da ya dace ne kawai domin PDP ta ci zabe, don kuwa APC ta kashe Jihar ta Edo. Kwamishinan na watsa labarai Tam-George, yace Gwamna Wike zai kara kuma dagewa wajen ganin PDP ta ci zabe domin ceto ‘yan Kasa.

Dakta Tam- George yace Nyesom Wike yayi kira ga mutanen Jihar Edo, da su tsaya tsayin daka wajen ganin sun zabi Jam’iyyar PDP. Ya kuma karyata maganganun da Gwamna Oshiomole ya furta na cewa Gwamna Wike da kuma takwarar sa, Ifeanyi Okowa na shirin murde zaben Jihar Edo.

Gwamna Adams Oshiomole dai ya zargi Gwamnonin yankin da hayar tsageru domin tada kayar baya, duk da bai kira sunan kowa ba.Wike

The post Karya ka ke yi Oshiomole-Kwamishinan Jihar Rivers appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.



from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2cl8WxS
// via IFTTT

No comments:

Post a Comment

Ads