Bisa ga daga zaben jihar Edo a ranan Alhamis 8 ga watan Satumba, wasu kungiyoyin farar hula karkashin lemar Situation room suna gargadin cewa demokradiyyan Najeriya ta shiga uku.
Jaridar Premium times ta bada rahoton cewa kungiyar ta bayyana hakan ne a wata jawabin da ta saki a ranan juma’a. Game da cewar kungiyar, yanke shawaran Hukumar INEC na daga zaben abun tuhuma ne, Hakazalika shawaran jami’an tsaro na cewan a daga.
Edo
Situation Room ta siffanta dagawan a matsayin ” abun damuwar rashin yarda da ma’aikatan gwamnati, ma’aikatu, da kuma matafiyar demikradiyya karkashin wannan gwamnati.”
“Wadannan abubuwa da suka faru sun tada tambayoyi da dama na saba dokan zaman kan Hukumar INEC da kundin tsarin mulkin ya bata, yin amfani da jami’an tsaro domin cima manufa ta kai, ya kasance cin zali da zurufin al’umman jihar Edo da kuma yan kasa da baki daya.” Jawabin yace.
KU KARANTA KUMA:Zaben Edo: PDP tawo hayar ‘yan daba- APC
“Muna taya mutanen jihar Edo juyayi akan wannan zalunci da aka yima demokradiyya . muna kira ga jami’yyun siyasa a jihar Edo da su shirya a sabon ranan zaben kuma su tafi cikin lumana.”
Clement Nwankwo ne ya samar da jawabin
The post Kungiyoyin farar hula na tausayawa demokradiyya karkashin Buhari appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2cMRxAm
// via IFTTT
No comments:
Post a Comment