Rushewar Tattalin Arziki: Abin sai da addu’a Inji Bukola Saraki
Shugaban Majalisar Dattawar Najeriya Dr. Abubakar Bukola Saraki tare da Shugaba Buhari da kuma Manjo-Janar Munguno (mai ritaya) a jiya bayan Sallar Juma’a
Shugaban Majalisar Dattawar Kasar nan Bukola Saraki, yace shi ma kan sa yana jin radadin wannan matsalar tattalin arzikin da ake ciki. Bukola Saraki yayi wannan magana ne bayan Sallar Juma’a inda suka yi sallah tare da Shugaba Muhammadu Buhari da sauran musulmi. Jaridar The Nation ta rahoto Shugaban Majalisar Dattawar yana cewa shi ma yana shan wahala kamar yadda kowa ke sha a Kasar!
Shugaban Majalisar Dattawar Kasar nan Dr. Bukola Saraki yace game da Rushewar Tattalin arzikin Kasar nan fa abin sai an hada da addu’a idan har ana so abubuwa su gyaru. Kuma kamar kowa shi ma yana cikin wannan radadi. Bukola Saraki yace kwanan nan za a fita daga matsalar rushewar tattalin arzikin Kasar nan.
KU KARANTA: An yaba da tsohon Shugaba Jonathan
Bukola Saraki yace idan aka dage da addu’a, kwanan nan za a fita daga cikin matsalar karayar tattalin arzikin da Kasar nan ta fada.
Saraki yace: “Inshaa Allahu za mu fita daga wannan matsala da muka samu kan mu, na karayar arziki. Abin da ya dace, shine mu dage da addu’a. Mu kuma marawa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari baya, idan Allah ya so abubuwa za su gyaru. Za kuma mu fita daga wannan matsala.”
Bukola Saraki yace wanda wannan lokaci na Arafat, za mu kara dagewa da addu’a, a ranar Lahadi, za mu roka ma Shugabannin mu, da su cigaba da yin abin da ya dace. Duk mu ma muna cikin wannan rikici da ya barke! Mun san abin da ke faruwa a Kasar.
Saraki yace babu dan Najeriyar da ke kishin Kasar sa da zai ji dadi game da abin da ke faruwa, don haka sai a dage da rokon Ubangiji. Mataimakin Shugaban Kasa ya dai ce kwanan nan za a fita daga cikin wannan matsala ta tattali.
The post Tattalin Arziki: Abin sai da addu’a-Bukola Saraki appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2cBD4Tf
// via IFTTT
No comments:
Post a Comment