Saturday, 10 September 2016

Osinbajo yayi magana akan durkushewar tattalin arziki

–Mataimakin shugaban kasa ,Farfesa yemi osinbajo ya bayyana zaton karewan nakasun tattalin arziki ba da dadewa ba

–Canji zai zo idan gwamnati tayi yaki da masu fasa bututun mai.

Professor Yemi Osinbajo, Nigerian's vice president

Professor Yemi Osinbajo

A makon da ya gabata, Cibiyar lissafin tarayya ta saki wani rahoto wanda ke nuna cewa najeriya na fuskantar durkushewan tattalin arziki.

Yayinda yake amsa tambayoyin yan Jarida a jami’ar Redeemers da ke Ede, jihar Osun, mataimakin shugaban kasa ya ba dadewa ba matsalan zai gushe.

Yayi bayanin cewa matsalan da ake fuskanta na faruwa ne sanadiyar dogaro da man fetur da kuma sace-sacen da gwamnatin da suka gabata sukayi.  Ya musanta maganan cewa durkushewan tattalin arzikin zai kai shekara 2020 kuma bayyana shirin najeriya na hada kai da masu sa hannun Jari domin gyara matatun man mu.

Yayinda ya ke magana ga kungiyar shugabannin bishops din arewa a Abuja, yace : “Babu kasar da zata fuskanci irin satan da akayi a najeriya ba tare da fuskanci matsala ba,harda na tattalin arziki. An yi biji biji da kasan, muna maganan an sace kudi $15 billion a bangare daya kacal.

KU KARANTA KUMA:Tattalin Arziki: Abin sai da addu’a-Bukola Saraki

“Duk da cewa bamu je bangaren man fetur ba inda tsohon gwamnan babban bankin kasa yace an sace $20 billion. Dole ne muyi yaki da rashawa. Wannan shine matsalan da muke fuskanta a kasan yanzu. Ba za mu iya mantawa da shi ba. Ba zamu ce saboda kirista ne ko musulmai mu manta da shi ba.

“An yi mumunan lalata kasar. Kudin mu na rage daraja saboda bamu da rara. Lokacin da ake samun kudin mai sosai, ba’a yi ajiya ba.

The post Osinbajo yayi magana akan durkushewar tattalin arziki appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.



from Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7 http://ift.tt/2cNg9I9
// via IFTTT

No comments:

Post a Comment

Ads